Labarai

Jiya an goge rainin Siyasa tsakanin Kauran bauchi da Dogara.

Spread the love

Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress a zaben cike gurbi na mazabar Dass a jihar Bauchi da aka gudanar a ranar Asabar, Bala Lukshi, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe.

Ana daukar zaben maye gurbin a matsayin zakaran gwajin dafi na karfin siyasa tsakanin Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, wanda kwanan nan ya sauya sheka zuwa APC.

Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ahmed Mohammed na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, wanda ya bayyana sakamakon, ya ce Lukshi ya samu kuri’u 12, 299 don kayar da babban abokin hamayyarsa na People’s Democratic Party (PDP) ), Lawal Wandi, wanda ya samu kuri’u 11,062 ya zo na biyu.

Don haka, ya bayyana cewa “dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Bala Lukshi, bayan da ya samu kuri’u mafi yawa an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma aka sake zabarsa.”

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa karamar hukumar Dass na daya daga cikin kananan hukumomi uku da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya wakilta.
Kujerun Mazabar Dass ta Rasa wakilci ne lokacin da ‘yan bindiga suka kashe wakilinta Musa Baraza a ranar Juma’a, 14 ga Agusta, 2020 a gidansa da ke Dass
Matan dan majalisar wadanda aka kashe, Rashida, Rahina, da ‘yarsa‘ yar wata 18, Khausar an sace su yayin harin amma ‘yan sanda sun cece su bayan sun kwashe kimanin kwanaki biyar a hannun masu garkuwar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button