Jonathan ya bani duk wata dama Amma nayi watsi dashi ~Ministan Buhari Ameachi.
Ministan Sufuri, Chibuike Amaechi, ya yi ikirarin cewa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ba shi duk wata damar da zai ci gaba da kasancewa a Jam’iyyar PDP, amma ya yi watsi da shi.
Ministan yace ya ci gaba da marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a 2015 saboda baya nuna kabilanci.
Tsohon gwamnan na jihar Ribas na magana ne a Fatakwal a ranar Asabar yayin da yake karbar wasu ‘yan jam’iyyar da suka sauya sheka daga PDP.
Bari in fada muku ko ni wane ne; Bana sha, ban taba shan giya a rayuwata ba, bana shan taba; Ba na nuna kabilanci. Ko a Jihar Ribas ko a Najeriya, ba na nuna kabilanci.
‘Idan na kasance mai nuna kabilanci, Shugaba Goodluck Jonathan ya ba ni dama na ci gaba da kasancewa a PDP, ya ba ni duk wata dama kuma na ce na yi wa Buhari mubaya’a saboda ban nuna kabilanci ba. Inji Minisatan