Rahotanni

Juyin Mulki: Sojojin Najeriya za su iya kwace Nijar cikin sa’o’i 13 kacal – Bashir El-Rufai

Spread the love

Bashir, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa sojojin Najeriya na iya kwace babban birnin Jamhuriyar Nijar, Yamai cikin sa’o’i 13.

El-Rufai ya nakalto wani faifan bidiyo da wani ma’abocin Twitter ya watsa yana yabon sojojin Jamhuriyar Nijar, El-Rufai ya ce baya fatan yaki amma yana da tabbacin sojojin Najeriya za su baje kolinsu tare da kwace Nijar cikin kasa da sa’o’i 13.

“Duba sojojin Tinubu suna son su je su yi fada da sojojin Najeriya,” in ji mai amfani da Twitter @chimaobi_nteoma.

El-Rufai ya mayar da martani: “Allah ya kiyaye yaki amma saboda faifan bidiyo irin na wauta ne nake fatan sojojin Najeriya za su baje kolinsu a Nijar su kama Yamai cikin sa’o’i 13.”

Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta yanke hulda da Najeriya bayan kokarin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta yi na maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ya ci tura.

Sakamakon haka, shugaban Najeriyar kuma shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, Bola Tinubu ya rubuta wa majalisar dattawan bukatar goyon bayanta ga tsoma bakin soja a kan mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

Rahoton Daily Post

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button