Labarai

Ka barni na ci gaba da Gina jam’iyar Apc a maimakon daukemin hankali da fastocinka a Abuja ~Ganduje fa’dawa Yahaya Bello

Spread the love

Shugaban Jam’iyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ta Bakin Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Felix Morka, ya bukaci tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, da ya baiwa kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje dama ya mayar da hankali wajen karfafa jam’iyyar, maimakon karkatar da ita ta Hanyar buga fostar kansa na neman Shugaban jam’iyyar na kasa.

A ranar Litinin din da ta gabata ne aka ga hotunan Bello a wasu sassan Abuja, lamarin da ke nuna sha’awarsa ta samun babban mukami a jam’iyyar.

An yi ta rade-radin rashin gamsuwa a tsakanin wasu jiga-jigan jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya wadanda rahotanni ke cewa har yanzu ofishin shugaban jam’iyyar na kasa da ke shiyyar zuwa yankin yana hannun wani dan Arewa maso Yamma.

Bayan ficewar Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa (Arewa ta Tsakiya) a watan Agustan da ya gabata, nan take Abdullahi Ganduje ya maye gurbinsa daga Kano (Arewa maso Yamma).

Yayin da Bello bai bayyana irin wannan buri ba, Morka ya ce babu wani gurbi a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, kuma ya tabbatar da biyayyar jam’iyyar NWC ga Dr Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button