Ka Canja Shuwagabannin Tsaro, Sakon Kungiyoyin Kare Muradun Yarbawa Da Inyamurai Ga Buhari.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Ana ci gaba da kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauke shuwagabannin tsaro saboda gazawa.
A jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin Arewa Maso Gabas da kuma shuqagabannin tsaro a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja.
A ganawar tasu shugaban kasar ya yabawa sojojin in yace Suna iya bakin kokarinsu amma dai ya yadda da cewa ya kamata su kara kokari.
Saidai da suke mayar da martani kan wannan lamari, kungiyar kare muradun yarbawa ta Afenifere ta bakin me magana da yawunta, Yinka Odumakin ta bayyana.
Itama dai kungiyar yarbawa ta YCE ta bakin me magana da yawunta, Kunle Oladije tace abinda suke tsammani shine shugaban kasar ya cewa shuwagabannin tsaron ya gode da aikin da suka yi sannan ya sallamesu.
Ya kara da cewa majalisa sun hi iya nasu tunda sun gayawa shugaban cewa ya saukesu. Hutudole ya ruwaito cewa Kunle yace amma binsa mamaki sai shugaban yayi biris da wannan kira.
Shima dai tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Oyo, Abideen Olaiya ya bayyana cewa kamata yayi shuwagabannin tsaron su canja salon yaki, hutudole ya samo cewa, dan siyasar ya gayawa Guardian cewa ana ta baiwa shuwagabannin tsaron kudi suna lakumewa ba tare da an samu nasarar da ake nema ba.
Shima Chuks Ibegbu, mataimakin me yada labaran kungiyar kare Muradun Inyamurai ta Afenifere ya bayyana cewa sojojin sun yi kokari amma akwai bukatar a kawo sabbin jini. Yace bada dadewa ba shugaba Buhari ya cewa sojojin bai gamsu da ayyukansuba, hutudole ya ruwaito cewa Afenifere tace shin wani abu ya canja game da tsaron? Dan haka kawai a canjasu shine mafita.
Itama wata kungiya ta YouthAid ta bakin me magana da yawunta, Smart Edward ta bayyana cewa, idan fa su sojojin basu gaji da Buratai ba ‘yan Najeriya sun gaji dashi.