Tsaro

Ka Daina Kashewa Sojoji Karfin Gwiwa Da Kalamanka, Hukumar Soji Ta Fadawa Gwamna Zulum.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Hukumar sojojin Najeriya ta gayawa gwamnan jihar Borno, Babagana Unara Zulum ya rika kiyaye kalamansa akan aikin sojojin saboda wasu kalaman na iya kawo hargitsi a tsakanin sojojin da kuma kashe musu karfin gwiwa.

A kwanakin bayane gwamnan ya fuskanci hari wanda aka zargi Boko Haram da kaiwa saidai gwamnan ya danganta harin da cewa zagon kasane na sojojin Najeriya.

Saidai a bayanin da yayi, bayan binciken sojoji akan lamarin, Mataimakin shugaban kwamandan rundunar Operation lafiya dole, Janar Felix Omoigui ya bayyana cewa zargin na gwamnan Borno ba gaskiya bane. Yace irin wadannan kalamai ka iya kawo matsala tsakanin Sojoji.

Yace kuma ana iya kaucewa wannan lamari idan da an kaiwa hukumar sojin korafi akan lamarin maimakon gayawa Duniya.

Da yake magana akan zargin cewa sojoji nmsun koma Noma a Maiduguri, Janar Felix yace hakan ba gaskiya bane saboda binciken da suka yi shine yawanci akwai bama-bamai binne a Baga tun bayan kwatota daga hannun Boko Haram.

Janar Felix yace bama-bamai 55 ne zuwa yanzu aka kwance a garin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button