Kungiyoyi

Ka Sa A Saki Mawakin Da Aka Yankewa Hukuncin Kisa A Kano, Sakon Wasu Sabbin Kungiyoyi 10 Ga Shugaba Buhari

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Maganar yankewa matashin Najeriya, Yahaya Umar Sharifai hukuncin kisa da wata kotun shari’ar musulunci a Hausawa, Kano ta yi na ci gaba da daukar hankula inda a yanzu wasu sabbin gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil’adama 10 sika nemi gwambatin tarayya data soke hukuncin kisan da akawa mawakin, bayan an sameshi da yiwa fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) kalaman Batanci.

Kungiyoyin sune committee of relevant Art, African Defenders,
Arterial Network Nigeria, PEN Nigeria,
Artistes and Risk Connection, Culture Advocate Caucus,
Human Rights Forum of Lead Africa International, Intro Africa, Freemuse, da kuma African Human Rights Network.

Sannan sanarwar ta kara da cewa wannan hukunci da akawa matashin ya take hakkin sa na dan adam na yin addini da yake so ba tare da tsangwama ba. Kaman yanda muka ruwaito muku cewa sanarwar ta nemi a baiwa Yahaya damar ganin Lauyansa da iyalinsa sannan a sakeshi.

Sanarwar ta kuma nemi gwamnatin tarayya ta soke duk wata dokar dake hukunta mutum akan batanci a kasarnan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button