Labarai

Ka saitaccan Tarihin labarin Dan Asalin Jihar katsina Abduljabbar surajo Guga.

Spread the love

AbdulJabbar Surajo Guga shine wanda ya assasa kuma yake jagorancin Gidauniyar nan ta Guga Global Foundation. A halin yanzu yana aiki a matsayin Daraktan Fasahar Sadarwa na Arewa maso yamma ayyukan lafiya a St Joseph, Missouri USA.

An haife shi cikin Iyalin Marigayi Alhaji Surajo Bawa Guga na Guga Village a Bakori LG na Kastina da kuma Hajiya Sa’adatu Ibrahim ta Daura, karamar hukumar Daura ta Kastina.

Ya halarci makarantu da dama ciki har da na islamiyya a Najeriya kafin ya koma Amurka don neman ilimi a Amurka 2007.

Ya yi aiki kuma ya sami ƙwarewa da yawa yayin tafiyarsa zuwa kasar Amurka, wanda ya faro daga ma’aikacin ɗalibai kuma a yanzu shi ne Daraktan Fasahar Bayanai na anungiyar Kula da Kiwon Lafiya ta Amurka.

Shi ƙwararren masanin Microsoft ne (MCPS) Microsoft Certified Solution Associate (MCSA) da sauran takaddun shaida na ITC.

Ya kasance mai alfahari da Al’ummar dake yankinsa kuma ya tsunduma cikin shirye-shiryen cigaban al’umma da yawa. A wani bangare na bayar da gudummawarsa ga ayyukan al’umma ya gina cibiyar kula da kwamfutoci a kauyensu na Guga a karkashin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Gidauniyar sa ta maida hankali wajen tallafawa marayu da kuma marasa karfi da gata a fadin jihar Katsina.
Wannan Gidauniya tana ayyukan taimako da jinkai, kamar kayan karatu da Rubutu na yara `Yan Nursery da makarantar firamare, da kuma rarraba kayan makaranta ga Daliban Secondary School, rabon kayan abinci, rabar da gidajen sauro da sauran ayyukan ci gaban al’umma, Alhamdulillahi an samu nasarar aiwatarwa tun lokacin da aka kafa Gidauniyar.

Abduljabbar surajo Guga, Shugaban Gidauniyar Guga Global Foundation Garkuwan Matasan kasar Hausa ya Karbi Kyautar Girmamawa Daga Kungiyar (Global Good Governors Ambassadors)

An karrama Abduljabbar surajo Guga Abisa Namijin kokarinda Gidauniyar shi ta Guga Global Foundation takeyi Babu dare babu Rana wajen taimakon Al’umma musamman marayu da marasa karfi Kuma haryanzu bai gajiyaba.

Abduljabbar surajo Guga, ya karbi Wannan Kyautar Girmamawa Daga Kungiyar (Global Good Governors Ambassadors) Bisa wakilcin Maitaimakinshi na Musamman akan yada labarai da hulda da Jama’a wato Comr. Bilyaminu Lawal Funtua.

Anyi Wannan Gagarumin taro ne a Babban Birnin tarayya (FCT) Abuja a Cikin Babban Dakin taro na Sharaton Hotel,Wanda ya gudana a Ranar Alhamiss dinda tagabata 05-Dec-2020.

Anbada Wannan Lambar yabone Domin nuna Godiya Ga Abduljabbar surajo Guga Abisa irin taimakon da yakeyiwa Al’ummar Jahar katsina Baki daya Daga Cikin Dukiyar da Allah ya hore Mashi.

Lambar yaboce wadda ta kunshi nasoriri da Dama a bangaren taimakon marayu da marasa karfi a fadin Nigeria bama jahar katsina kadai ba,Domin Gidauniyar tana fadada ayyukan ta bangarori daban-daban na taimakon Al’umma musamman marayu da marasa karfi.

https://asguga.com
Instagram: Abdul_Guga
Twitter: Abdul_Guga

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button