Labarai

Ka sauka a mulki ka koma gefe idan ba zaka iya kawo karshen matsalar ta’addanci ba a Nageriya ~Atiku ya Fa’dawa Shugaba Tinubu.

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya tunkari shugaban kasa Bola Tinubu kan matsalar tsaron kasar nan, musamman matsalar garkuwa da mutane da ake yi a fadin kasar nan.

Atiku, wanda ya fafata da Tinubu a zaben shugaban kasa a 2023, ya roki shugaban kasar da ya koma gefe idan ba zai iya shawo kan matsalar rashin tsaro da ke kara tabarbarewa a kasar nan ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce duk da karuwar al’amura na rashin tsaro, shugaban na iya samun karfin gwiwa ya bar kasar ya kuma kai wata ziyarar sirri a Faransa.

Atiku ya ce kasar ba ta bukatar wani “Babban Bakin Zirga”.

A makon jiya ne Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa domin wata ziyarar sirri.

Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya bayyana hakan a wata sanarwa mai taken ‘Shugaba Tinubu ya tafi kasar Faransa.

Ko da yake sanarwar ba ta bayyana dalilan ziyarar ba, Ngelale ya ce, “zai dawo kasar a makon farko na watan Fabrairun 2024.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button