Ka Yi Hankali Da Masu Zanga-zangar ENDSARS, Ina Ga Akwi Boyayyar Manufa Aciki – Shugaban APC Ya Gargadi Buhari.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya gargadi gwamnatin Buhari da tayi taka tsan-tsan game da zanga-zangar da ke faruwa a duk fadin kasarnan.
Gwamnan ya ce akwai yiwuwar wata boyayyiyar manufa a bayan zanga-zangar adawa da ‘yan sanda masu yaki da fashi da makami (SARS) a duk fadin kasarnan.
Buni wanda yake magana a wata hira da sashen Hausa na BBC, ya ce akwai bukatar gaggawa ga shugabanni a dukkan matakai su hadu don kawo karshen zanga-zangar kafin ta yi waje.
“Idan aka kalli zanga-zangar a yanzu, sai kace wani abu mara kyau ya buya.
Duk da matakan da gwamnati ta dauka kan bukatun masu zanga-zangar, har yanzu suna kan tituna suna zanga-zangar.
Dole ne gwamnati tayi taka tsan-tsan da su.
“Me kuma masu zanga-zangar suke so?
IG ya dauki matakin gaggawa. Don haka, ina ganin ya kamata su dakatar da zanga-zangar su hau teburin tattaunawa da gwamnati don a samu mafita, ”inji shi.
Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki a daidai lokacin da kasar ke fuskantar babban kalubale, yana mai jaddada cewa ba za a iya daidaita Najeriya a cikin shekaru biyar ba.