Siyasa
Kada Fa Ka Ci Zabe Ka Koma APC Fayose Ya Fadawa Gwamna Obaseki.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya gargadi gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki cewa kada ya ci zaben gwamna yace zai koma APC.
Obaseki wanda bayan da ya fadi zaben fidda gwanin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya koma PDP inda suka bashi takara a yanzu haka basa ga maciji da tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole.
Nan da kasa da makonni 5 ne ake sa ran za’a yi zaben jihar Edo. Da yake bayyana ra’ayinsa akan lamarin, Fayose ya gargadi gwamna Obaseki ta shafinshi na sada zumuntar Twitter cewa, ya girmama alkawarin da yayi da PDP.
Yace shi ba mutumin Oshiomhole bane sannan kuma baya tare da Gwamna Obaseki amma yana masa fatan Allah yasa ya ci zabe.