Siyasa

Kada kuyi ƙasa a gwiwa wajen mikawa jam’iyar PDP mulki idan lokaci ya yi, gwamna Wike ya fadawa jam’iyar APC.

Spread the love

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya gargadi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kada ta yi gardama a lokacin da za su mikawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mulki a 2023.

Gwamna Wike ya kuma jaddada cewa ‘yan Najeriya suna jiran PDP ta dawo kan mulki.

Mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya bayyana hakan a wata sanarwa bayan kaddamar da wasu ayyukan jihar.

Wike ya kuma shawarci Ndume da APC da su mutunta bukatun ‘yan Nijeriya bayan babban zabe mai zuwa.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button