Siyasa

Kada Kuzo Wajen Zabe Da Takunkumin Fuskar Da Yake Dauke Da Tambarin Wata Jam’iyya — INEC Ta Gargadi Masu Kada Kuri’a…

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

A daidai Lokacin da Zabubbukan Gwamnoni a Jihohin Ondo Da Edo Suke Kara Karatowa, Wadanne Ake Saran Gudanarwa a Ranakun 19 Ga Watan Satumba, Dakuma 10 Ga Watan October, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC Wanda Ita take da Hurumin shirya Zabubbukan, ta Bukaci Daukacin Masu Kada Kuri’a a Jihohin Guda Biyu Dasu kiyayi Sanya Takunkumin Fuskar Da Yake Dauke da Tambarin Wata Jam’iyyar Siyasa ko Wani Dantakara a Lokacin da Zasu Halarci Rumfunan Kada Kuri’a,

Kwamishina kuma Shugaban kwamitin Hukumar kan Harkokin Kada Kuri’a tareda Sarrafawa, Farfesa Okechukwu Ibeanu ne yaja kunnen Masu Kada kuri’ar a Jiya Laraba a Birnin Tarayya Abuja, a tattaunawa ta farko da Kwamitin Yayi da Manema Labarai Dangane da Zabubbukan Jihohin Ondo Da Edo.

Inda Muka Jiyo Farfesan yana Cewa “Sanya Takunkumin Rufe Fuska Wajibine Ga Kowanne Mai Kada Kuri’a da yaziyarci Rumfar Zabe Domin Kada kuri’arsa, Amma Dukkannin Wanda yaziyarci Rumfar Zabe da Takunkumin Fuskar Da Yake Dauke da Tambari ko Hoton Wata Jam’iyyar Siyasa ko Dan takararta, to Babu Shakka Za’a Bashi Umarnin komawa Gida Domin yacireshi, Tareda Sabunta Wani, Wanda Baya Dauke Da irin Wadannan Hotuna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button