Kada Mutum Ya Bari Wani Matsayi Na Wucin Gadi Yasa Shi Ya Kasa fadarsa Gaskiya, Martanin Salihu Tanko Yakasai Ga Ganduje..
Tsohon mai bawa gwamnan Kano shawara Salihu Tanko Yakasai ya mai da martani ga gwamnatin Kano bisa tsigeshi da akai.
Gwamnatin Kano ta tsige Salihu Tanko Yakasai, Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Comrade Garba Shehu shine ya sanar da dakatar da Salihun saboda wasu kalamai da yayi akan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Salihu Tanko Yakasai dai ya yi dan tsokaci ne game da batun yin gum da shugaba Buhari yayi akan kiraye kirayen ‘yan Najeriya akan Rundunar ‘yan sanda mai yaki da fashi da amakami, wato SARS.
Salihun ya yi tsokacin ne ta shafinsa na Twitter, inda ya siffanta Gwamnati ta Shugaba Buhari da mara mara tausayi.
Jim kadan bayan tsokacin nasa gwamnatin ta Kano ta sanar da korarsa daga mukaminsa na mai bawa gwmna Abdullahi Umar Ganduje shawara akan yada labarai.
A Martanin da ya mayar bayan cireshi, Yakasai ya ce “Kada Mutum Ya Bari Wani Matsayi Na Wucin Gadi Yasa Shi Ya Kasa fadarsa Gaskiya.
Daga Kabiru Ado Muhd