Kafin mu sauka a Mulki Zamu kaddamar da Titin Abuja Kaduna da Kano dukda cewa bamu kammala aikin ba ~ Shugaba Buhari.

Gwamnatin Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya Bakin Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola (SAN) ya bayar da tabbacin cewa za a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar kafin ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Sai dai ya ce za a ci gaba da aiki a bangare daya na aikin na Kaduna-Abuja, ko da bayan gwamnatin Buhari saboda ba za a yi katsalandan a cikin kudaden da ta ke ba.
Ministan ya yi wannan jawabi ne a garin Zaria na jihar Kaduna a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya a rangadin aikin titin sashe na biyu da na uku.
Ya ce, “Mun yi alkawarin kai wannan aiki kafin karshen wannan gwamnati kuma da yardar Allah za mu yi hakan.
Sashe na biyu (Kaduna-Zaria) mai nisan kilomita 73, za a kammala shi kafin karshen wannan makon kamar yadda dan kwangilar ya tabbatar, yayin da za a kammala sashe na uku (Zaria-Kano) a wata mai zuwa,” inji shi.