Kakakin Majalisar Jihar Borno ya karyata Minista watsa labarai Lai Muhammad.
Kakakin Majalisar Jihar Jihar Borno, Hon. Abdulkadir Lawan Guzamala, ya Karyata Ministan Watsa Labaran Najeriya, Lai Muhammad, da Tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaron Kasar (CDS) Janar. Gobriel Olonisaki, kan Ikirarin da Sukayi na Cewa Duk kan Kananan Hukumomin Jihar Borno 27 din suna Cikin ‘yan cinsu karkashin kulawar Soji.
Hon. Guzamala, yace Karamar Hukumarsa da yafito yake wakilta a Zauren Majalisa, Ma tana Karkashin Ikon Boko Haram, sama da shekaru 3 Shi ma bai Isa ya shiga karamar Hukumar ba, kawo yanzu Duk yankin Babu Kowa.
Yace “Duk da kokarin da Gwamnan Jihar yayi na ganin Kowa ya koma garinsa amma Wannan al’amari bai yiwuba.
“Mutum yana Abuja yana zaune cikin Aminci, yana zuba karyar cewa Kowa yana Zaune Lafiya alhali Ba haka bane.
Guzamala, yayi kira ga Sabon Shugaban Hafsoshin Tsaron kasar Nan, Janar Leo Irabo, da cewa ya Taimaka musu a Inganta Tsaro a Yankin dama Jihar Domin Masu Zaman Gudun Hijira su koma Hidajesu.
“Kananan Hukumomi 10 dake arewacin jihar Har yanzu Suna Cikin Tashin Hankaline, yace Kasar Nan nada Kananan Hukumomi 774 Kodai Gwamnatin Tarayya ta Cire Karamar hukumar Guzamala ne daga Cikinsu?
Kakakin Majalisar yayi wanna Maganar Ne a wajen Taron ( Guzamala Concerned Stakeholders Meeting) Jiya Litinin a Maiduguri, a Wajen da ‘Yan Yankin suke Zaman Hijira.
Ahmed T. Adam Bagas ✍️