Kalaman Batanci Ga Sanata Uba Sani APC ta Buƙaci a hukunta Kakakin dokokin Majalisar jihar kaduna ~wato Hon Zailani Yusuf.
Shugabannin jam’iyyar All Progressive Congress, (APC) na kananan hukumomi bakwai da suka hade yankin Kaduna ta Tsakiya sun yi kira da’a sanya takunkumi ga kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Zailani da abokinsa, Chakis Sakamakon saba wa doka ta 21 sashin A) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Idan baku manta ba dai an kama kakakin majalisar Zailani da Chakis a cikin wani bidiyo a kwanan nan suna maganganun batanci da kalamai marasa kan gado game da Sanatan da ke wakiltar gundumar Kaduna ta Tsakiya Sanata Uba Sani, wanda shugabannin APC Suka dauka a matsayin Kalaman Batanci marasa kyau kuma illa ga jam’iyyar.
Bayan tashi daga taro a ranar Juma’a, shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomi bakwai Wanda Suka hada da, Gambo Shehu Haske, Alhaji Ibrahim Musa, Engr. Magaji Bala Mataz, Alhaji. Abdulahi Jariri, Alhaji Ibrahim Yakubu Soso, Alhaji Musa Sheriff da Hon. Ishaya Shagay, sunce Shugaban Majalisar da Chakis sun tsallake layi tare da maganganun da suka jawowa jam’iyyar zama abin kunya.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun dukkan shugabannin APC na kananan hukumomi bakwai na Chikun, Kaduna ta Kudu, Kaduna ta Arewa, Birnin Gwari, Igabi, Giwa da Kajuru bayan taron da suka yi a Kaduna, sun yi Allah wadai da kalaman tare da yin kira da a sanya takunkumi ga Shugaban Majalisar Zailani da Chakis.
Sanarwar ta ce: “Sashi na 21 A) na Kundin Tsarin Mulki na Jam’iyyar ta APC ya bayyana laifukan su da kuma hukuncin su kuma abin da su biyun suka yi ya dace da laifukan karamin sashe na 1, 11, V da VII.
Shugabanin sun Kara da Cewa Dangane da abin da ke sama, mu shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomi bakwai na Kudancin Kaduna ta Tsakiya suka ce mun cimma matsaya kan cewa ya kamata a dauki matakan ladabtarwa a kan Kalaman da Hon. Zailani Yusuf da Hon. Aliyu Haruna Chakis sukayi a dukkan matakai, ”inji su.
Shuwagabannin Jam’iyyar sun ce sabanin ikirarin da Zailani da Chakis ke yi, Sanata. Uba Sani ta hanyar ofishinsa ya ba da dama da kuma nemawa tare da ba da rance ga jama’arsa: “Sanatan ya kuma bai wa mazabarsa karfin gwiwa ta hanyar aikin gidauniyar Uba Sani, wanda matasa da yawa suke aiki a ciki kuma mata da dama suke anfana da irin abubuwan da yakeyi.
“Sanata Uba Sani ya yi rawar gani a cikin shekara daya ta hanyar daukar nauyin wasu kudirai wadanda ke da nufin inganta rayuwar wadanda suka zabe shi. Sanata Uba Sani yana Kan aikinsa na bayar da gudummawar kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya a karamar Hukumar Giwa, Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya da ke Rigasa wacce ke karkashin karamar hukumar Shugaban Majalisar Yusuf Zailani, kudirin ya wuce karatu na uku kuma yana jiran amincewar shugaban kasa da sauran kudurin da za su kawo ci gaban da aka rasa a yankin Sanatan.
“Sanatan ya kawo ayyuka da yawa wanda Igabi ke amfana da Ginin Kwalejin a Jami’ar Jihar Kaduna Wacce za’a Gina a darajar Naira Biliyan 2.4, da kuma samar da dakunan kwanan dalibai masu karfin 110bed a Kwalejin’ Gwamnati ta ‘Yan Mata dake Giwa da ta Sakandaren Gwamnati Birning Gwari.
“Ya kuma dauki nauyin gina Cibiyar Kwarewar na’ura Mai kwakwalwa kimanin 50000 a Birnin Gwari, Giwa, Kaduna ta Kudu da Kaduna ta Arewa. Gina Cibiyar Samun Kwarewa a Karamar Hukumar Chikun da kuma Cibiyoyin Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko a Kasuwar Magani, Kajuru. Duk a cikin shekara Daya inji ”shugabannin na APC.