Siyasa

Kalaman Wauta PDP kwankwasiyya ta buƙaci hukuma su dau matakin gaggawa Kan Abdullahi Abbas.

Spread the love

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta lura da wani faifan Video na shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC Abdullahi Abbas da yake ta yawo a kafafen sadarwa na zamani wanda a cikin faifan Video ɗin shi wannan mutumin ya ƙara fito da al’adarsa ta rashin kunya, kalaman tunzuri tare da wauta wanda ya sha aikata irin hakan a baya.

A cikin wannan faifan Video mun jiyo shi shugaban riƙon na APC yana kalaman wauta kamar haka:

  1. Yana faɗin cewa lokacin da za’ayi zaɓe bisa gaskiya da adalci ya wuce a jihar Kano.
  2. Zasu tabbatar da cewar sai an sake zuwa zaɓen Inconclusive a shekarar zaɓe ta 2023.
  3. Ya zama dole Jam’iyyar APC ta cigaba da riƙe madafun iko tun daga sama har ƙasa.
  4. Ba zamu taɓa bari ayi zaɓe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba sannan sai mun tabbatar hukuma ta bayyana zaɓe a matsayin wanda bai kammala ba sannan zamuyi murɗiyar zaɓe kamar yadda mukayi a Gama.
  5. Ina kira a gareku da kada ku taɓa ɗagawa kowanne Ɗan Kwankwasiyya ƙafa.

A baya dai bamu fiya ɓata lokacin mu ba a duk lokacin da shi wannan mutumin yayi kalaman sa da ya saba yi na wauta da yunƙurin tayar da fitina, a wannan karon ma bai kamata mu ɓata lokacinmu mu tanka masa ba amma munga dacewar mu sanar da duniya wasu muhimma abubuwa kamar haka:

  • Waƴannan kalaman na wauta tare da yunƙurin tayar da tarzoma babbar shaida ce da alamu da suke nuna cewar hatta makaho wanda baya gani zai iya fahimtar cewa Jam’iyyar APC ba jam’iyya ce mai so a ɗabbaƙa tsarin Dimokaraɗiyya ba. Sannan wannan babbar shaida ce da take nuna cewar lallai sun tabbata masu tayar da hargitsi tare da yin ayyukan ta’addanci kamar yadda kowa ya sani. Sannan sun fito da aniyar da suke da ita na yiwa tsarin Dimokaraɗiyya kutungwila domin kawai su tabbata akan mulki ta kowacce siga.

Idan akayi la’akari da abubuwan da suka faru da waƴanda kefaruwa sannan a haɗa da kalaman wautar da Abdullahi Abbas yayi zamu iya cewa:

  1. Zaɓen gwamna 2019 Engr. Abba K. Yusuf ne yayi nasara da rinjaye mai yawa kafin daga bisani Ƴan fashin zaɓe su ƙwace masa zaɓensa ta hanyar mayar da zaɓen wanda bai kammala ba (Inconclusive).
  2. Duk wani hargitsi da tayar da zaune tsaye wanda akayi a wajen kammala zaɓe (Inconclusive) jam’iyyar APC da shirya hakan.
  3. Ko kaɗan jam’iyyar APC bata yin wani shiri domin tunkarar zaɓen 2023 da nufin yin zaɓe bisa gaskiya da adalci, su dai kawai burinsu 2023 su sake maimaita abin da ya faru a 2019.

Saboda haka muke kira ga al’ummar jihar Kano masu albarka musamman ƴaƴan jam’iyyar PDP da su zama cikin shiri, masu bin doka da kuma juriya da dukkanin wani nau’in tsoratarwa da jam’iyya mai mulki zata zo muku da shi.

Hakanan kuma muna tunatar da al’ummar gari ku sani wawayen mutane masu gurɓatacciyar dabi’a tare da zuciya mara son zaman lafiya basu cancanci kuri’unku ba a kowanne mataki, sannan ya kamata al’umma suyi watsi da su kada su ƙara bari waƴannan mutanen suyi amfani da wata hanya wacce ba ta Dimokaraɗiyya bace domin kawai su ƙara dafe madafun iko.

Mu dai a kowanne lokaci cikin shiri kota kwana muke domin mu ƙalubalanci duk wata barazana tasu da sukeyi a garemu ta hanyar aiki ko magana kodai ta wata siga da zamu iya fuskanta daga jam’iyyar APC ko gwamnatin APC domin muga mun kare haƙƙoƙinmu na yin zaɓe, yin nasara tare da tabbatar da nasarar a duk lokacin da buƙatar haka ta taso.

Daga Ƙarshe muna kira ga Kwamishinan Ƴan sanda na jihar Kano, Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya da dukkanin sauran mutanen da alhakin samar da tsaro ya rataya a kansu da su tabbatar sun ɗauki wannan kalaman da wannan mutumin yayi suyi nazari a kai domin yin abin da ya kamata akan wannan kalaman na wauta da yunƙurin tayar da hankali.

Haka nan muna kira ga ɓangaren shari’a, Kwamishinan hukumar zaɓe na jihar Kano, su saurari abin da wannan mutumin ya faɗa dangane da zaɓen 2019 da kuma irin mugun tanadin da suke yiwa 2023 Wanda jam’iyyar PDP ba zata taɓa lamunta ba ko kaɗan.

Hon. Shehu Sagagi
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button