Kamfanin Barker Hughes na Amurka zai gina matatar mai a Najeriya
Kamfanin mai na Amurka, Barker Hughes, ya nuna sha’awar sa hannun jari a matatun mai a kasarnan, a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta kara zage damtse wajen kawo karshen shigo da man fetur daga kasashen waje.
Najeriya, kasa ce mai arzikin danyen mai, tana shigo da dukkan albarkatun man fetur daga kasashen waje, lamarin da ya sanya matsin lamba ga kudinta a kasuwar canji.
Amma da yake magana a yayin ganawarsa da karamin ministan albarkatun man fetur (man) Sen. Heineken Lokpobiri, a gefen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya (COP28) karo na 28, Mista Lorenzo Simonelli, Shugaba na Baker Hughes. sun nuna matukar sha’awar ci gaba da habaka jarin da suke zubawa a masana’antar mai da iskar gas a Najeriya, gami da shirye-shiryen saka hannun jari a matatun mai.
Wata sanarwa da mai taimaka wa ministar kan harkokin yada labarai, Nneamaka Okafor ya fitar, ta ce taron na jiya ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin gwamnati na jawo hankalin masu zuba jari a harkar man fetur da iskar gas.
Simonelli ya isar da kudurin Baker Hughes na ba da gudummawa ga tsarin canjin makamashi na gwamnatin Renewed Hope, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.
Ya jaddada shirin kamfanin na yin hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya wajen inganta ayyukan makamashi mai dorewa, daidai da manufofin COP28.
Simonelli ya ce: “Najeriya kasa ce mai albarka wadda ke da fa’ida da dama a bangarori daban-daban. A matsayinmu na abokin tarayya da gwamnatin tarayya tsawon shekaru, an bamu kwarin guiwa kan saka hannun jari a fannin matatun mai da iskar gas.
“Saboda haka, duk abin da za mu iya yi don tallafawa don farawa, a shirye nake in yi hakan, ko da a yanzu.”
A nasa martanin, Sanata Lokpobiri ya yabawa katafaren kamfanin na duniya bisa dadewar hadin gwiwa da Najeriya ta yi a fannin makamashi.
Ya bayyana irin gudummawar da kamfanin ya bayar a tsawon shekaru tare da nuna kyakkyawan fata game da zurfafa hadin gwiwar ta hanyar kara zuba jari a masana’antar mai da iskar gas ta kasar.
Sanata Lokpobiri ya tabbatar wa tawagar Baker Hughes kudirin gwamnatin tarayya na samar da yanayi mai kyau na saka hannun jari a bangaren matatun mai.
Ya tabbatar da cewa za a samar da isassun matakan da za su saukaka aiwatar da tsare-tsaren saka hannun jari na Baker Hughes ba tare da wani cikas ba, wanda ya yi daidai da ra’ayin gwamnati.
“Na yi matukar farin ciki da kuka shiga wasu kamfanoni wajen gano manyan damammaki da manufofin gwamnati a bangaren man fetur da iskar gas da kuma zuwan PIA, yanzu muna da tsarin aiki wanda zai ba da tabbacin yanayi mai kyau don saka hannun jari,” in ji shi.