Labarai
Kamfanin jigilar kayayyaki na Danish, AP Moller-Maersk na shirin zuba jarin dala miliyan 600 a Najeriya
Kamfanin jigilar kayayyaki na kasar Denmark, A.P Moller-Maersk ya bayyana shirin zuba jarin dala miliyan 600 a Najeriya domin daukar karin ayyukan jigilar kayayyaki a tashoshin jiragen ruwa na Najeriya.
Shugaban Cibiyar A.P Moller-Maersk, Mista Robert Maersk Uggla, ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da shugaba Bola Tinubu a gefen taron tattalin arzikin duniya na musamman kan hadin gwiwar duniya, ci gaban da makamashi don raya kasa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya ranar Lahadi. .
Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa, wannan jarin zai taimaka wajen zuba jarin dalar Amurka biliyan daya da gwamnatin ke yi na sake gina tashar jiragen ruwa a sassan gabashi da yammacin kasar ta Najeriya.