Kasuwanci

Kamfanin NNPC Ya bukaci masu ababen hawa da su kwantar da hankalinsu akan batun kara kudin man fetur.

Spread the love

Sabanin rade-radin da ake yi game da karuwar farashin Man Fetur a kasar nan, Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, ya ce ba za a kara wani karin farashin na man fetur a watan Maris, 2021 ba.

Wata sanarwa da mai magana da yawun NNPC, Kennie Obateru ya fitar, ta ce kamfanin ba ya tunanin karin farashin mai a cikin watan Maris don kada ya kawo cikas ga ci gaba da yin aiki tare da kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki kan tsarin da ya dace, wanda hakan zai wahalar da talakawan Najeriya.

Kamfanin na NNPC ya kuma gargadi dillalan man fetur da kada su kara farashin mai ba bisa ka’ida ba ko kuma boye man fetur domin su haifar da karancin man na wucin gadi, wanda hakan zai wahalar da talakawan Najeriya.

Kamfanin ya bayyana cewa yana da isasshen mai na man fetur wanda zai wadatar da kasar sama da kwanaki 40.

A karshe Kamfanin ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su kara sa ido kan ayyukan ‘yan kasuwar tare da hukunta wadanda suka kara farashin man fetur ba bisa ka’ida ba ba.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button