Kimiya Da Fasaha

Kamfanin Revival Technology Suna Cigaba Da Samun Makudan Kudade Da Hannun Jarin Miliyoyin Daloli Saboda Yunkurinsu Na Samar Da Wata Fasaha Da Zata Iya Dawo Da Wanda Ya Mutu Duniya.

Spread the love

Wannan kimiyyar ta yunkurin dawo da matacce duniya ta samo asali ne daga wani Malamin Physics a kwalejin Michigan Mai suna Robert Ettinger a shekarar 1976 a birnin Michigan na kasar Amurka.

Yanda fasahar za tayi aiki shine da zarar mutum ya mutu za’a dauke shi a saka gangar jikinsa a cikin wani abu “Vaccum” ayi sanyaya shi yanda zai dauki tsawon shekaru ba tare da wani bangare na jikinsa ya lalace ba.

Ana ajiye gawar mutum ne da zummar duk lokacin da aka gama bincike za’a dawo dashi duniya ya cigaba da rayuwa da wasu sinadarai na “Nano Technology” wanda yanzu haka ake bincike akansu.

A yanzu haka akwai sama da mutum dubu shida wanda suka biya makudan kudade da zummar duk lokacin da suka mutu a ajiye gawarsu har sai an gama binciken yanda za’a dawo dasu duniya a inda wasu kuma suka biyawa yan uwansu wadanda sun jima da mutuwa.

Idan zaku iya tunawa a kwanakin baya na yi wani rubutu akan yanda wani kamfani a kasar Amurka ya tara masana da zummar hana mutuwa kwata-kwata tare da karawa mutane lafiya da tsawon rai har kusan shekaru goma .

Karshen duniya ya zo 🥲… Amma menene yasa kuke ganin turawa suka Fara yin wannan binciken?

Usman Umar Dagona FASF.
13-05-2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button