Kan Zagin Buhari A Facebook Wani masoyin Buhari ya maka abokinsa na Facebook A Kotu.
Wani masoyin Shugaba Muhammadu Buhari Mai suna Sani Ahmad Zangina ya maka wani abokinsa na facebook Mai suna Ardo Shehu a kotu Kan zagin da yayi Masa ya Kuma zagi Shugaba Muhammadu Buhari ta uwa ta uba a shafinsa na Facebook Lamarin daya hassala sani Zangina ya garzawa Zuwa Kotun Upper Area Court Dake lafiya Jihar nasarawa.
Da Farko dai Sani Ahmad Zangina yayi shiyarin din wani labarin ra’ayinsa da Gidan jaridar Mikiya ta wallafa Masa Izuwa shafinsa.
Ra’ayin na Zangina da gidan jaridar Mikiya ta wallafa shine Kamar Haka..
Masu Cewa Baba Buhari Ya Sauka Shin idan Ya Sauka To Yanzu Waye muke dashi da zai iya rike Amanar Rayuwarmu kamar Buharin?
Daga Sani Ahmad Zangina
Ka Sauka! Ka Sauka!! Ka Sauka!!
Kayi Murabus! Ka yi Murabus!! Ka yi Murabus!!!
Ka kaddara baba Buhari ya yi murabus yau! Wanene kake tunanin ya maye gurbinsa?
Waye za ka iya damkawa amanar kula da rayuka da dukiyoyin ka a matsayin shugaban kasa?
Idan kana ganin kamar Buhari ya gaza da yadda yake jagorantar wannan kasar, to ya kamata ka shirya zama shugaban kasan Najeriya nan gaba ta hanyar buga fastocin ka da niyyar tsayawa takarar mukamin sa a shekara ta 2023 in Allah ya kaimu.
Zaka iya fahimtar hakan inka fito tallar hajarka ta yarda, gaskiya da rikon amana sannan ka fahimci cewa Baba Buhari alkairi ne.
Fatan alheri ga Baba Buhari da fatan Allah ya yi masa jagora.
Barka da Juma’a gare ku baki daya.
wannan shine ra’ayin sani Ahmad Zangina
Ga Kuma zagin da shi Ardo Shehu yayi kamar Haka..
Don kutumal ubanka inya mutu babu wonda zai iya mulkin kasannan Kennan , ubangiji Allah ya kwace maka albarka, jahilin banza akwoi Dubai da sukafi munafikin bakin arnennan tsohon banza kaji.
Kawo yanzu an kawowa Ardo Shehu sammaci Amma Ardo Dake zaune a mararaban Abuja Da Jihar Nasarawa Yace yayi tafiya Zuwa jihar kaduna.
Alkali zai Fara sauraron shari’ar a Ranar 16 ga wannan wata na Disamba da muke Ciki…