Kankara: Mai yiwuwa Buhari ne ya tura yara ‘yan makaranta zuwa yawon bude ido ga ‘yan ta’adda – Oby Ezekwesili.
Tsohuwar Ministar Ilimi, Oby Ezekwesili, ta yi ikirarin cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gudanar da aikin sace yara maza sama da 300 daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kankara, Jihar Katsina.
Ezekwesili, tana magana ne a gidan Talabijin na Channels, ta dage kan cewa bai kamata a jinjina wa Buhari ba saboda sakin daliban bayan kwanaki shida a tsare.
Tsohuwar ministar, wanda tana daya daga cikin wadanda suka hada kan kungiyar ‘Bring Back Our Girls’ wacce ta jagoranci zanga-zangar neman ceto ‘yan mata‘ yan makaranta sama da 250 daga Chibok a jihar Borno, ta nemi Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya bayanin abin da ya faru a Kankara.
Satar ta auku ne ‘yan sa’o’i kadan bayan Shugaban ya isa garin Daura, Katsina a ranar 11 ga watan Disamba don ziyarar sirri ta mako guda.
“Don mu taya gwamnatin da ta haifar da matsala kuma ta ce ta warware ta? Bai kamata mu yi haka ba. Al’umma su koyi yadda zasu yiwa mutane hisabi. Waɗannan yara an saka su cikin haɗari. Yanzu kuma ya ce ya kubutar da su? Wataƙila Shugaban ya tura yaran ne zuwa yawon buɗe ido ga ‘yan ta’adda don su iya sakin yaran yadda suka ga dama da shi.
“Muna bukatar ya fada mana ainihin abin da ya faru da yaran Kankara. Akwai matsala. Bai kamata kasar nan ta hau kan Shugaba Buhari da gwamnatinsa ba. Wannan bashi da kyau kuma duk duniya suna mana dariya. Suna ganin mu masu wasa ne. Yawancin kasashe ba su ma damu da nuna cewa wani abu ya faru a kasarmu ba saboda sun ji su waye wadannan mutanen kuma me suke yi wa kansu? ” Ezekwesili ta ce.