Kansiloli Sun Tsige shugaban ‘Karamar hukumar kombotso A jahar Kano
Majalisar Kansiloli ta ‘Karamar Hukumar Kombotso, Ta Sanar Da Dakatar da Zababben shugaban ‘Karamar hukumar honorable Kabiru Ado Panshekara, Bisa Zarginsa na Almundahanar wasu ‘Kudade na ‘Karamar Hukumar.
Shugaban Majalisar Kansilolin shine yasanarda haka Acikin wata takarda da Aka rabawa manema labarai A Kano, inda suka bayyana shugaban ‘Karamar hukumar da Aiwatar da wasu Ayyuka batareda sahalewar Majalisar tasu ba dakuma fitar da wasu ‘Kudade A matakin ‘karamar hukumar, batare da Sun sani ba wanan Dalilin ne yasa Suka Dakatar dashi Har tsawon watanni Uku.
Shugaban ‘Karamar hukumar ta Kombotso Honorable Kabiru Ado Panshekara, An zargishi da karkatar da tallafin cobid-19 da jahar Kano ta Raba A ‘kananan hukomomi har takai ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano ta Gurfanar dashi A Gaban Kotu.
Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano