Labarai

Kara Farashin fetir da tsadar Kayan Abinci shike Kawo ta’addancin Nageriya -kwankwaso

Spread the love

Tsohon gwamnan na Kano ya ce baya goyon bayan wadannan matakai na gwamnati musamman a lokacin da mutane ke fama da matsaloli iri-iri. Ko Wacce Kasa a Duniya tana kokarin Kawo Tsare tsaren da zata taimaki al’ummarta Amma Banda Nageriya yakamata Nageriya ta Kawo tsarin da zai Hana kudin zirarewa ne Amma ba saka al’ummarta a wahala ba.

“Duk wanda ke wannan kasa ya san da cewa wannan ba lokaci ne na dorawa mutane wannan nauyi ba, don haka ma’anar hakan shi ne sabuwar yunwa da sabuwar matsalar tsaro da sabon rashin aikin yi da dai matsaloli iri-iri da zasu biyo bayan wannan mataki na gwamnatin Najeriya” a cewar Kwankwaso.

Tsohon gwamnan ya ce idan har gwamnatin Buhari na sauraron jama’arta, to yakamata idan tayi abu ba dai-dai ba to ba abun kunya bane ta gyara don a samu ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

” Ita harkar gwamnati akwai maganar kudin shiga akwai kuma maganar kudin da ake kashewa, don haka abin da ake a irin wannan yanayi shine sai a duba aga wadanne kofofi na barna za a toshe, domin akwai hanyoyi da yawa da gwamnati zata iya kawo gyara a kan irin barnar da ake yi”.

Ya ce “Da irin wannan mataki gwamnati ta bi, da ‘yan kasa sun yi murna, sannan sun kuma ji dadi domin kowa abin da yake so shi ne ya samu rayuwa mai kyau”.

Kwankwaso ya ce, bisa la’akari da irin arzikin da Najeriya ke dashi, ba sai anje an dauki wasu matakai da za su dada hargitsa tsarin tattalin arzikin kasar ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button