Kasuwanci

Karancin Naira: CBN ya umurci bankuna su bude ranar Asabar, Lahadi

Spread the love

Babban bankin na CBN ya kuma tabbatar da kwashe takardun kudi daga rumbun ajiyarsa zuwa bankunan kasuwanci a fadin kasar nan domin saukaka zirga-zirgar kudaden.

Babban bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da kwashe takardun kudi daga rumbun ajiyarsa zuwa bankunan kasuwanci a fadin kasar, a wani mataki na hadin gwiwa na ganin an sassauta yaduwar takardun banki na daban-daban.

Babban bankin na CBN ya kuma umarci dukkan bankunan kasuwanci da su bude aiki a ranakun Asabar da Lahadi.

Mukaddashin Daraktan Sashen Sadarwa na Babban Bankin na CBN, Isa AbdulMumin ne ya bayyana hakan a Abuja, ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa an samu makudan kudade a bangarori daban-daban da bankunan kasuwanci suka karba domin mikawa abokan huldarsu.

A cewarsa, babban bankin na CBN ya umurci dukkan bankunan da su yi lodin ATM dinsu tare da gudanar da ayyuka na zahiri a dakunan banki a karshen mako.

“Babban bankunan kasuwanci za su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi don biyan bukatun abokan ciniki,” ya kara da cewa gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, zai jagoranci kungiyoyin da kan sa ido kan matakin da bankunan ke bi a wurare daban-daban a fadin kasar.

Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri domin halin da ake ciki zai samu sauki nan ba da dadewa ba tare da yin allurar wasu takardun kudi a wurare daban-daban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button