Karfin Kuzari na ne yayi kasa shiyasa na tafi hutu zan dawo na karbi rantsuwa ba tare da kasala ba ~Cewar Bola Tinubu.
Da yake magana ta Bakin Jam’iyyar ta kuma ce zababbun shugaban kasar, wanda ya bar Najeriya a hukumance tun ranar 22 ga Maris, zai dawo nan gaba kadan gabanin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Kasa, Felix Morka ya yi magana a cikin shirin Siyasa na Yau na Channels Television a ranar Alhamis.
Da aka tambaye shi game da inda zababben shugaban kasa yake, kakakin jam’iyyar APC ya ce, “Shi (Tinubu) yana nan lafiya. Bayan zaɓen da duk ƙarfin kuzarin sa yayi kasa, kawai ya yanke shawarar ɗaukar ɗan karamin lokaci domin Hutu.
“Da zarar ya dawo aka rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, ba za a yi kasala ba, za a dora masa nauyin tafiyar da kasa mai girma da sarkakiya kamar Najeriya.
“Na san zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.”