Labarai
Karin Farashin fetir, Iftila’i ne ya faru a Gwamnatin Buhari ~Muaz Magaji
Batun Karin Farashin man fetir da Gwamnati ta aiwatarw Tsohon Kwamishinan Ganduje Muaz Magaji win-win Yace Duk sanda ka ji an leko ko raderadin sabon batu ko wani sabon tinani ko tsari na Gwabnati …to ana gwada zurfin ruwa ne….idan akaji shiru to sai a aiwatar….idan ko a ka ji yan kasa sun tashi tsaye sun yi kememe sai kaji an fasa …sai ace dama ba gaskiya bane! Kaga an tsira kenan…
Ni da naji 212 sai na dauka ma biredin ne Gwamnatin Tarayya zata rabawa talakawan dake fama da matsananciyar rayuwa a wannan halin da ake ciki…Ashe wani iftilain “Jiki Magayi” ne ya kara fado wa talaka!