Karin Kudin Lantarki Dana Mai: Ya Kamata Al’umma Su Gane Gwamanti Ba Sadaka Tafito Yi Ba, In Ji Tsohon Sarkin Kano Sunusi Π.
Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cire tallafin man fetur.
Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na karin kudin shan wutar lantarki da man fetur abu ne mai kyau.
Ganin halin tattalin arzikin da aka shiga a sakamakon annobar COVID-19, Malam Sanusi II ya ce ya kamata a gane gwamnati ba sadaka ta fito yi ba.
Jaridar Punch ta rawaito Muhammadu Sanusi II ya na cewa gwamnati ba za ta iya cigaba da abin da ta ke a kai mai kama da rabon goron kirismeti ba.
A dalilin annobar COVID-19, tattalin arzikin Najeriya ya durkushe, ina tunanin yanzu dole Najeriya ta fuskanci ainhin halin da ake ciki.
Mu na biyan biliyoyin daloli da sunan wani tallafi, damfara ce kurum wanda aka yi shekaru 30 ana yi, Inji tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan.
A yan watannin bayan nan, gwamnati ta kawo gyare-gyaren da idan aka cigaba da tafiya a haka, za a kai ga ci, Cire tallafin man fetur ya na cikinsu.
Daidaita farashin man fetur daya daga cikinsu ne.
Sanusi II ya yabawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ya ce dama ace tun tuni aka yi wannan, wadannan gyare-gyare da ya kamata ayi.
Mu na bukatar mu fahimci cewa gwamnati ba ta da karfin da za ta cigaba da wannan sadaka da kudi.
Ya ce babu maganar biyan tallafin man fetur a cikin kasafin kudin da ta aikawa majalisa.
Daga Comr Haidar Hasheem Kano