Labarai

Karin Kudin Mai: Shugaban Kasa Ya Fahimci Wahalar Da Talakawa Ke Fuskanta, Yana Kokarin Samar Musu Saukin Rayuwa, Cewar Yemi Osinbanjo

Spread the love

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce shirin da Gwamnatin Tarayya za ta yi na sauya motocin yan Najeriya su yi amfani da Manfetur Gas za su fara da motocin kasuwanci.

Ya ce tuni aka fara shirin a jihar Edo inda ya ce kamfanin Dangote ya sauya manyan motoci 4,000 don yin amfani da gas.

A cewar wata sanarwa a ranar Litinin ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Laolu Akande, Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi.

Wannan na zuwa ne kimanin wata guda bayan da aka kara farashin mai da wutar lantarki a kasar.

Sanarwar an yi mata taken “Shugaban kasa ya fahimci wahalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta, yana kokarin samar da karin nasara a cewar Mataimakin Shugaban Kasar Yemi Osinbajo

An ambato Osinbajo yana bayyana shirin a matsayin daya daga cikin dabarun da Gwamnatin Tarayya ke bi don ganin ta ragewa yan Najeriya makamashi cikin sauki don gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Ya ce, daya daga cikin hanyoyin ita ce ta hanyar amfani da iskar Gas.

Gwamnati ta jajirce don yin tuban. Da farko dai, muna farawa da motocin kasuwanci.

Mataimakin shugaban kasar ya ce a yanzu haka gwamnati na bin wasu hanyoyi don rage radadin da ke kan ‘yan Najeriya, yana mai cewa babu wanda ya yi tsammanin faduwar tattalin arzikin kasar nan sakamakon faduwar annobar COVID-19.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button