Labarai
Karka kara mana radadin da tashin farashin man fetur, Dattawan Yarbawa sun fadawa Tinubu
Majalisar Dattawan Yarbawa, YCE, a jiya, ta bayyana damuwarta kan halin da al’ummar kasar ke ciki, kamar yadda ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya magance wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
YCE, a cikin wata sanarwa da babban sakatarenta, Oladipo Oyewole, ya fitar, ya ce duk da cewa ana fatan za a samu sauyi mai kyau a kasar, “a halin yanzu, akwai wahala da yawa a kasar.”