Kasashen Ketare

Karka Kuskura Ka Kara Tsoma Mana Baki A Cikin Harkokin Mu Na Cikin Gida___Shugaban Kasar Mali Ya Gargadi Shugaba Buhari.

Spread the love

Shugaban kasar Mali kanal Sadio Camara ya gargadi shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari akan kada yakara tsoma musu baki a cikin harkokinsu Na cikin gida.

Kanal Sadio Camara yace kasar Mali ba kasar Najeriya bace, kasar Mali daban kasar Najeriya daban, don haka su sukasan mawuyacin halin dayasa suka hambarar da gwamnatin farar hula a kasar su.

Kanal Sadio Camara yakara da cewa basuyi juyin mulki a kasar su ta Mali ba seda suka samu tabbacin goyon bayan talakawan kasar su ta Mali Wanda hakan ne ya tabbatar musu da cewa talakawan kasar Mali sun gaji da mulkin tsohon shugaban kasar Mali Bubacar Kaita, basajin dadin mulkin.

Kanal Sadio Camara yace don haka shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yaguji tsoma baki a cikin al amuran da bashi da hakikannin sanin gaskiyar abinda yake boye.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button