Labarai

Kar’mutun yayi zaton irin hakurin-mu daya da tsohon gwamna Masari ~Cewar Gwamnan katsina Dikko Radda.

Spread the love

Gwamnan jihar katsina Dr Umar dikko Radda ya bayyana hakan ne a wajen taron walimar bankwana da tsohon gwamnan jihar katsina Rt hon Aminu bello masari Radda yana mai cewa tun daga lokacin da allah ya hadani da Mai Girma Gwamna ubanmu Alh Bello masari harya Zuwa wannan lokaci da muke a yau duk gurbin da Allah ya kaini akwai hannunsa a ciki kuma Haryanzu da Allah ya bani wannan mukami ba fasa bani shawara ba Bai fasa gaya mani Gaskiya ba irin wacce kowa Bai iya gaya mani.

Abu Daya da nake so na tabbatar WA Mai girma Gwamna Insha Allah ba zan baka kunya wajen Cin amanar mutanen katsina ba zan kokari Bakin gwargwado na tsare mutuncin mutanen jihar katsina zan tsare dukiyoyin su Ina kira ga Al’ummar jihar katsina suyi hakuri gyara dole sai Rai ya baci.

Duk Kasar nan duk fa’din jihar katsina idan akace Aminu bello masari za’a ce An San mutun ne Mai hakuri kar mutane suyi zaton irin hakurin mu Daya dashi Inji gwamna Dr Radda 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button