Labarai

Kasa A Dakatar Da Sabuwar Dokar Hana Zagin Shuwagabanni SERAP Ta Bukaci Shugaba Buhari

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Kungiyar dake saka ido akan harkar gudanar da gwamnati ta SERAP ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya sa Ministan yada labarai, Lai Muhammad da hukumar kula da kafafen yada labarai, NBC su dakatar da dokar hana zagin shuwagabanni.

Kungiyar a sanarwar data fitar cikin wata budaddiyar wasika ta bayyana cewa wannan matakin doka yayi karan tsaye ga ‘yancin fadar albarkacin baki. Mun samo cewa SERAP ta bukaci shugaban kasa da kuma ya dakatar da harajin da akawa gidan rediyon Nigeria Info na Miliyan 5.

An kakabawa Nigeria Info wannan haraji ne saboda yanda ta bar tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya yayi zargin cewa akwai gwamnan Arewa dake kwamanda a Boko Haram.

SERAP ta ce maimakon wannan doka marar ma’ana, kamata yayi gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta sa wakilan gwamnatinta su rika karfafa al’adar bayyana bayanan ayyukan gwamnati.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button