Tsaro

Kasa Da Mako Daya Da Kashe Kanar Bako A Borno, ‘Yan Ta’addan Katsina Sun Kashe Wani Kanar Din Sojan.

Spread the love

Sojojin Najeriya sun rasa wani babban hafsan hafsoshin soja daya (wanda aka ruwaito Kanar ne) da sojoji biyu.

Birgediya Janar Benard Onyeuko, mai rikon mukamin Daraktan, Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, kamar yadda jaridar DAILY POST ta rawaito a yau Juma’a.

A ranar Alhamis, sojoji a kan aikin kawar da masu aikata laifuka a duk yankin Arewa maso Yamma sun sami bayanai game da harin ‘yan fashi a kauyen Unguwar Doka, karamar hukumar Faskari na jihar Kastina.

Onyeuko ya ce jami’an Operation SAHEL SANITY sun ba da agajin gaggawa, kuma sun tafi zuwa yankin.

“Sun yi nasarar tsarkake ƙauyen daga masu fashin, sun kwantar da hankalin mutanen yankin.

A yayin arangamar, sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan fashi 21 yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi cikin dajin kamar yadda aka nuna ta hanyar jinin da ke kan hanyar tserewar masu aikata laifin.

“Dakarun sun yi nasarar kubutar da mutane 3 da aka yi garkuwa da su ciki har da jariri dan watanni 8 da ke tsare a hannun masu laifin fiye da kwanaki 23.

A yayin farmakin, sojojin sun kwato bindiga kirar AK 47 guda daya, da kuma babura 3 daga hannun ‘yan ta’addan.

“Abin takaici, sakamakon arangamar da aka yi da ‘yan ta’addan, wani hafsan soja daya da sojoji 2 sun rasa rayukansu, yayin da wasu sojoji 2 suka ji rauni, a halin yanzu suna karbar magani a asibiti, likitoci kuma suna ba su kulawa mai kyau.”

Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun ci gaba da bin ‘yan ta’addan zuwa cikin dajin tare da mamaye yankunan baki daya tare da sintiri na fada don hana su wani jinkiri.

An bukaci Sojojin da kada su huta, har sai sun tsakake yankin daga dukkan masu aikata laifi.

Onyeuko ya ba da tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyi ya kuma karfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwa su ba da bayanai kan lokaci kuma sahihi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button