Ilimi

Kasa Tana Girma Ne Idan An Habbaka Fannin Iliminta — Dan Majalisar Tarayya..

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Nnewi North, Nnewi South dakuma Ekwisigo a Majalisar Tarayyar Kasarnan, Dr. Engr. Chris Emeka Azubogu, Yabayyana Cewar Babu wata Kasa dazataci Gaba Matukar Bata Mayar Da Hankali Fagen Inganta Fannin Ilimin Kasar ba.

Yakara Da Cewar Zuwa Makaranta Yana Taimakawa Al’umma Fagen Ganin Sun Fuskanci yadda Tsarin Rayuwa yake Tareda Fahimtar yadda Zasu Habbaka tattalin Arzikin Kasa, Tareda Nasu Tattalin Arzikin,

Sannan Dan Majalisar Tarayyar yakoka Bisa Yadda Makarantun Gwamnati a Kasarnan Suka Lalace Tareda Fita daga Hayyacinsu Inda ya Bukaci Gwamnati Datayi Kokarin Gyarasu Duba Da Yadda Sune Suke Daukeda Kaso mafi Tsoka Na Daliban Kasarnan.

Jami’ar Nsukka (UNN) ce Dai Ta yaye Wannan Engineer kuma Dan Majalisa, wadda yakeyin Jawabi Akan yadda Za’a baiwa Kowanne Yaro Ingantacce kuma Nagartaccen Ilimi a Fadin Kasarnan batare Da Nuna Banbanciba .

Musani Ilimi Hasken Rayuwane Kuma Shine Gishirin Zaman Duniya,

A Don Haka Muna Kira Ga Gwamnatin Tarayyar Kasarnan data Habbaka Fannin Ilimin Kasarnan Domin Anan Gaba a Saka Najeriya Daga Cikin Jerin Kasashen Duniya Da Suka Samu Cigaba, Wanda Hakan Shine Mafarkinmu a Kowacce Rana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button