Kasafin Kudin 2021 Nayi matukar Jinjinawa Shugaba Buhari bisa ga bawa fannin Noma Lafiya Ilimi Fifiko Cikin kasafin~Inji Sanata Uba Sani.
A Zaman Majalisa Na yau Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya ya Yace A yau, na sami damar bayar da gudummawa ga muhawara kan ka’idojin Kasafin Kudin shekarar 2021 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar
Zama yayi kyau sosai Na yaba wa Gwamnatin Tarayya kan fifiko ga fannoni masu muhimmanci kamar ilimi, kiwon lafiya da noma, sannan kuma ta mai da hankali kan kammala ayyukan da ke gudana a maimakon fara wasu sabbi.
Gyara gibin kayayyakin more rayuwa babbar hanya ce ta farfado da tattalin arziki da kuma sanya kasar kan turbar ci gaba mai dorewa.
Na yi kira ga Shugaban kasa da ya tsawaita ga bankin CBN da ke kula da kudin ruwa kashi 5 cikin dari wanda aka kebe shi zuwa ga Micro Small and medium enterprises (MSMEs) daga nan zuwa watan Disamba na 2021. Wannan zai ba gwamnati damar isa ga wasu masu cin gajiyarta kuma ta kawo taimakon da ake buƙata ga su MSME wanda annobar COVID-19 ta shafa. Za a baiwa kananan manoma wata hanyar rayuwa da sake basu kuzari don bayar da gudummawa yadda yakamata don cimma nasarar wadatar da abinci a Najeriya.
Inji Sanata Uba Sani Sanatan Kaduna ta tsakiya..