Kasashen Ketare

Kasar Amurka Ta Sanya Takunkumin Biza Ga Wasu ‘Yan Siyasa Masu Magudin Zabe A Najeriya.

Spread the love

Kasar Amurka karkashin ikon Shugaba Donald Trump ta sanya takunkumin biza ga wasu ‘yan siyasar Najeriya da aka samu da yin magudin zabe don biyan bukatun kansu.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Morgan Ortagus wanda wanda ya kasance mai magana da yawun Ma’aikatar Gwamnati cewa, an sanya takunkumin biza ga mutanen da suka yi magudin zaben jihar Kogi na 2019 da na jihar Bayelsa.

Ta kuma bayyana cewa, baya ga sanya dokar hana biza a kan jihar Kogi da Jihar Bayelsa da ke magudin zabe, Amurka ma tana kallon zabubbukan da za a gudanar a jihar Edo da Ondo, kuma duk wani dan siyasa da aka samu yana murde zaben shi ma za a dakatar dashi.

Ta ce Amurka na yin hakan ne domin tallafawa Gwamnatin Tarayyar Najeriya a yakin da take yi na kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button