Labarai

Kasar Eritiriya Ta Sanar Da Kawo Karshen Cutar Korona A Fadin Kasar.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Eritiriya sun bayyana cewa gwmnatin kasar a hukumance ta sanar da kawo karshen cutar Korona Virus da ta Addabi Duniya , bayan da dukkan mutane 39 da suka kamu da cutar suka warke kuma aka sallame su daga Asibiti kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta bayyana.

Ya zuwa 8 ga watan mayu da muke ciki, mutane 2 ne kawai suka rage dake dauke da cutar a kasar, ind aka sallami daya daga cikinsu a ranar 11 ga watan, sai kuma na karshe da aka sallama a jiya Juma’a, yanzu dai ta bi sahun kasashen Murtaniya da Maurishius wajen kakkabe cutar baki daga daga kasashensu.

Daga lokacin bullar cutar a kasar mutane 39 ne kawai suka kamu da ita, kuma dukkansu sun warke an sallamesu babu wanda ya rasa ransa daga cikinsu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button