Kasar Indiya ta zama Kasa ta farko da ta fara Saukar da Jirginta a duniyar wata Kuma kusa da wata.
Kasar Indiya ta bi sahun manyan kungiyoyin kasashe da suka saukar da jirgin saman su a duniyar wata, bayan Amurka, USSR da China Chandrayaan-3 ya sauka cikin nasara, kwanaki hudu bayan gaza sauka da Jirgin Rasha ya yi.
Da karfe 14:34 na lokacin tsakiyar Rana a Turai, Indiya ta shiga cikin rukunin kasashe na musamman da suka saukar da jirgin sama a duniyar wata, bayan Amurka, USSR da China. Kusan mintuna 20 a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, kasar ta ci gaba da kasancewa cikin kyakykyawan zato.
Duk idanu suna kan Jirgin India Mai suna Chandrayaan-3, wanda Vikram lander ya fara gangarowar sa a hankali zuwa ga kusa da wata. Kumbon, wanda a hankali ya yi tafiyar hawainiya, a karshe ya sauka a hankali kusa da sandar kudu, yankin da har yanzu ba a taba nano shi ba tun farkon Duniya, da kuma wani ci gaba a tarihin shirin sararin samaniyar Indiya.
Wannan shi ne ƙoƙari na biyu. A cikin 2019, manufa ta farko ta Indiya ta gaza bayan da wannan Ya shiga kewayen wata, amma ta rasa tuntuɓar ƙungiyar a Duniya.
An yi ta murna da tafi a Bangalore ranar Laraba daga cibiyar kula da binciken sararin samaniya ta Indiya (ISRO). Sama da mutane miliyan 7 ne kuma suka bi saukar ta kusa da wata kai tsaye a tashar su ta YouTube ta ISRO. Firayim Minista Narendra Modi daga Johannesburg, inda ya halarci taron BRICS (Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu) ya ce “Nasarar da kasar Indiya ta samu a duniyar wata ba wai ta Indiya kadai ce ba.” “Wannan nasarar ta dukkan bil’adama ce,” in ji shi, yana mai karawa da cewa “Zai taimakawa ayyukan duniyar wata da wasu kasashe ke yi a nan gaba.”