Addini

Kasar Ingila Zata Bibiyi Shari’ar Wanda Yayi Batanci Ga Annabi (s.a.w), Ta Ce Abar Kowa Yarika Fadin Ra’ayinsa.

Spread the love

Kasar Ingila Ta Yi Allah Wadai Da Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Yiwa Annabi (SAW) Batanci A Kano Inda Tace Tana Bibiyar Lamarin.

Kasar Ingila a karin farko ta yi magana akan hukuncin kisan da aka yankewa Yahaya Umar Sharifai na kisa bayan samunsa da laifin yiwa annbi kalaman batanci.

Tace ta yi Allah wadai da hukuncin sannan kuma tana nan tana bibiyar yanda lamura ke gudana akan yanke hukuncin. Mun ruwaito muku Yanda aka yankewa Yahaya hukunci a kotun shari’ar Musulunci dake Hausawa, Kano.

Kasar ta bayyana cewa, ya kamata a bar kowa ya rika bayyana ra’ayinsa kan duk wani lamari ba tare da takura ba. Sannan tace tana inkari kowane hukuncin kisa.

Ta bayyana bakane a martanin tambayar da jaridar Punch ta aikewa ofishin jakadancin ta na Najeriya inda me kula da yada labaran ofishin jakadancin, Christopher Ogunmodede ya bayyana haka.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button