Labarai

Kasar Iran ta Fara Shirin kamo Shugaban Amurka Trump Kan zargin kisan Janar Qassem Suleiman.

Spread the love

Tehran ta aika wa Interpol neman izinin sammacin kasa da kasa na neman shugaban Amurka Donald Trump dangane da kisan babban janar din Sojan kasar ta Iran Qassem Soleimani shekara guda da ta gabata.

Kakakin shari’ar Iran Gholam Hossein Ismaili ne ya bayyana hakan a gidan talabijin din Iran ranar Talata

Yace Game da wannan, mun gabatar da sanarwa’ a Interpol kan mutane 48, da suka hada da Donald Trump da wasu, kwamandojin Amurka, da wakilan Pentagon da kuma sojojin Amurka,” in ji Ismaili.

Kakakin ya kara da cewa, akwai hadin gwiwa mai ma’ana tare da makwabciyarta Iraki kan batun..

A ranar 3 ga Janairun 2020, bisa umarnin Trump, Sojojin Amurka sun kashe Soleimani, wanda ke ziyarar Iraki tare da harin roka kusa da filin jirgin saman Baghdad.

An kuma kashe shugaban mayakan sa kai na Iraki Abu Mahdi al-Mohandes, da mataimakin shugaban kungiyar mayaƙan Hashd al-Shaabi na Iraki.

Soleimani shi ne kwamandan fitattun sojojin Quds, wani bangare na fitattun sojojin Iran.

Ya tsara ayyukan mayaka masu biyayya ga Iran a Iraki da sauran kasashe.

Shugaba Hassan Rowhani ya kira Soleimani a matsayin gwarzo na kasa kuma ya zama sananne a yankin bayan kisan da Amurka ta yi masa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button