Labarai

Kasar Iran Ta Tsare Mutum 42 Bisa zarginsu Da Bautawa Shaidan.

Spread the love

Kasar Iran ta bada umurnin tsare wasu Mutane su 42 bisa zarginsu da bautar shaidan.

Kamfanin dillancin labarun kasar Iran mai suna IRNA shine ya bayyana cewa an Kama mutane 42 a Garin chalus bisa zarginsu da bautar shaidan.

Mutanen sun hada da mata 14 yayinda sauran kuma suka kasance dukkan su maza ne.

A wannan farmakin anyi nasarar kwace motoci 11 daga hannun masu bautar shaidan din, wanda aka tabbatarda mallakin masu bautar shaidan din ne.

Haka kuma jami’an leken Asiri a kasar Iran din sun kama wani mutum da ake kyautata zaton shine limamin masu bautar shaidan din.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button