Labarai
Kasar Ireland Zata Dawowa Da Najeriya Wasu Kudin Abacha

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Kasar Ireland zata dawowa da Najeriya kudaden da tsohon shugaban kasa, Marigayi Sani Abacha ya kai bankin kasarta.
Tsohon shugaban kasar da ya mulki Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998 an ti ta dawo da kudaden da ya kai kasashen waje tun bayan da ya mutu.
Kwatankwacin wadannan mudi a Naira sun fi Biliyan 2. Ministan shari’a ta kasar Ireland din, Helen Mcentee ta bayyana cewa zasu dawowa da Najeriya kudadenne saboda girmama dokokin kasa da kasa.
Kaman Yanda Aka ruwaiti muku cewa a shekarar 2014 ne aka yi alkawari tsakanin Najeriya da kasar ta Ireland cewa za’a dawo mata da kudin.