Siyasa

Kasar Rasha Ta Mayarwa Da Shugaban Amurka Donald Trump Martani Kan Batun Yakin Duniya Na II.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta ayar wa Trump da martani kan ikirarin da ya yi dangane da samun nasara a yakin duniya na biyu, inda ya ce Amurka da Burtaniya ne suka samu nasara.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitara shafinta na twitter, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta bayyana cewa, abin mamaki ne yadda Trump ya ya kebance nasarar da aka samua kan Nazi a lokacin duniya na biyu ga kasarsa da kuma Burtaniya kawai.

Ta ce abin mamaki ne matuka wani furuci irin wannan ya fito daga wani mutum wanda yake da masaniya kan yadda aka yi yakin duniya na biyu da kuma yadda ya gudana, da kuma yadda aka yi nasara kan sojojin Nazi na Jamus.

Kafin haka dai wasu jami’ai da daban-daban na gwamnatin Rasha sun mayar wa Trump da martani, inda suke kiransa da ya koma ya sake karanta tarihin yakin duniya na biyu kafin ya furta wata magana a kansa.

Inda suke bayyana furucin na Trump da cewa ya yi hannun riga da abin da ya faru a lokacin yakin, domin kuwa sojojin tarayyar Soviet ne suka fattataki sojojin Hitler na Jamus, tare da kora su har cikin birnin Berlin, inda suka kwace iko da birnin, wanda hakan ya tilasta Hitler tsrewa, daga lokacin ne kuma sojojin Nazi suka mika kai ga sojojin tarayyar Soviet.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button