Kasashen Da Suke Taimakawa ‘Yan Gudun Hijira Da Sunan Jinkai Sai Sun Cutar Dasu Sau 9 Kafin Su Amfanar Dasu Sau 1, Inji Dr. Khalifa Dikwa.
Rufe Kofa Da Barawo A Lamuran Tsaron Arewa Maso Gabashin Najeriya Da Ake Yi Da Sunan NGOs.
Masanin tsaro Dr. Khalifa Dikwa yace Kasashen da suke taimakawa kasashe masu fama da yake-yake suna taimakon su ne ta hanyar cutar dasu sau 9 a fakaice, sai su amfanar dasu sau 1 rak- Inji Masanin tsaro Dr. Khalifa Dikwa.
Yayi jawaban ne albarkacin bikin da aka gudanar na ranar “Zaman Lafiya ta duniya” wacce majalisar dinkin duniya ta ayyana, wanda bikin ya gudana a wannan sati.
.
Sannan kuma ya kara da cewa kasashen suna yin hakan ne ta yadda zasu dinga samun kudade idan kasashen da suke fama da yaki sun sayi makamai a hannun su, ya kuma kara da cewa kuma suna satar albarkatun kasar da suke fakewa da taimakon su.
Ko a kwanakin baya ma dai an zargi wasu kungiyoyin agaji (NGOs) suna kara iza wutar rikicin boko haram da sunan taimakawa al’umma, kungiyoyin NGOs dai suna bada tallafi na abinci, da magunguna, da sutura, da kayayyakin karatun dalibai, da kudi, da dai sauran su ga al’ummar da suka tagayyara, kuma suke neman dauki a saboda dalilai na fatattakar su da ‘yan bindiga suke yi daga gidajen su na haifuwa.