Lafiya
Kasashen Duniya Na Fargabar Dawowar Corona Virus karo Na biyu…
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Sakamakon fargabar sake bullar cutar tasa an kulle kasuwannin Dillalan Kayan Abinci shida a Beijing babban birnin China, Kuma an sake dage Lokacin komawa makarantu.
A wannan makon ne dai aka Sassauta Dokar kulle a kasar India sai dai a kulli yaumin akan samu Karin mutane masu dauke da Cutar a Kasar.
A Korea kuwa an dauki matakan kariya da kamuwa da Cutar da Muhalli domin Gudun yawaitar Cutar.
A Rasha kuwa Akwai fargabar Sake Barkewar Anobar kasancewa Kasar Itace ta Uku wajen masu Yawan Cutar a Duniya.
A Nageria ma dai Duk da Sassauta dokar da Akayi a kulli yaumin Ana samun Karuwar masu dauke da Cutar kamar yadda Hukumar dake kula da Cututtka masu yaduwa ta Kasar NCDC take Sanarwa kullum.