An rantsar da Shugaba Yoweri Museveni a matsayin Shugaban ƙasar Uganda a karo na shida.

Shugaban Yoweri Museveni ya kama aiki a matsayin Shugaban ƙasar Uganda karo na shida a jere.

Shuwagabannin ƙasashe 11 ne suka halarci bikin rantsuwar wanda ya gudana jiya Laraba a babban birnin Kampala.

Bayan rantsuwar kama aiki, Shugaba Museveni yayi alƙawarin cigaba da kyautata rayuwar mutanen Uganda kamar yadda suka amince dashi da kuma ƙara zaɓar sa.

Yoweru Museveni mai shekaru 76 a Duniya, ya zama Shugaban ƙasar ta Uganda ne a shekarar alif 1986 tun daga nan kuma haryanzu shike kan karagar mulkin ƙasar.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *