Da alama Salman Rushdie marubucin da yayi ɓatan ga Annabi zai rasa ido, kuma hantarsa ​​ta yi rauni tare da lalacewa sakamon harin da aka kai masa a birnin New York na kasar Amurka

“Labarin ba shi da kyau. Da alama Salman zai rasa ido daya; jijiyoyin da ke hannunsa sun yanke, kuma hantarsa ​​ta yi rauni tare da lalacewa,” in kakakinsa.

Salman Rushdie, marubucin da yayi batanci ga Annabi an dora shi a na’urar hura iska bayan an kai masa hari da wuka a jiya juma’a.

Andrew Wylie, mai magana da yawun Mista Rushdie, ya ce a cikin wata sanarwa a yammacin ranar Juma’a cewa an sanya marubucin a na’urar hura iska kuma ya sami raunuka masu yawa.

“Labarin ba shi da kyau. Da alama Salman zai rasa ido daya; jijiyoyin da ke hannunsa sun yanke, kuma hantarsa ​​ta yi rauni tare da lalacewa,” in ji sanarwar.

Mista Rushdie yana magana ne a wani taron da aka gudanar a cibiyar Chautauqua da ke yammacin New York, lokacin da wani mutum da ake zargin ya hau kan dandalin ya afkawa Mista Rushdie da wani mai magana.

“Da misalin karfe 11 na safe, wani mutum da ake zargi ya haye kan wajen inda ya kai hari ga Rushdie da wani mai magana. Rushdie ya ji rauni a wuyansa, kuma an dauke shi da jirgi mai saukar ungulu zuwa wani asibitin yankin,” in ji sanarwar ‘yan sanda.

Daga baya ‘yan sandan sun bayyana wanda ake zargin da sunan Hadi Matar, dan shekara 24 daga New Jersey.

Gwamnan New York, Kathy Hochul, yayin wani taron manema labarai ya yaba wa Mista Rushdie saboda jajircewarsa, duk da barazanar da ake yi wa rayuwarsa.

“Yana da rai, an dauke shi a jirgi zuwa asibi. Amma ga wani mutum da ya kwashe shekaru da yawa yana fadin gaskiya ga mulki, wanda ya kasance a can baya jin tsoro, duk da barazanar da ta biyo bayan rayuwarsa gaba daya,” in ji Ms Hochul.

Tun bayan da yayi rubuta Littafin batanci ga addinin Musulunci Mista Rushdie ya boye tsawon shekaru tara.

Littafin ya tayar da hankalin musulmai, saboda sabon da yayi aciki, kuma an haramta shi a wasu kasashen musulmai. A cikin 1989, Jagoran addinin Musulunci na Iran Ayatollah Khomeini ya yi alkawarin tukuicin $3m (£2.5m) ga duk wanda ya kashe shi.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na fadar White House, Jake Sullivan, ya ce harin da aka kai wa Mista Rushdie ya kasance “mai ban tsoro”, yana mai cewa a shafin Twitter: “Muna godiya ga ‘yan kasa nagari da masu ba da taimako na farko da suka taimaka masa cikin sauri.”

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “A cikin shekaru 33 da suka gabata, Salman Rushdie ya alamta ‘yanci da yaki da duhu. Kiyayya da dabbanci sun same shi, don hakan na da matsorata. Gwagwarmayarsa tamu ce kuma ta duniya baki daya. Yau fiye da kowane lokaci muna tare da shi” in ji Macron

Leave a Reply

Your email address will not be published.